Shugaba Buhari ya caccaki tsohon Shugaban Kasa Obasanjo akan rashin Wutar Lantarki

Shugaba Buhari ya caccaki tsohon Shugaban Kasa Obasanjo akan rashin Wutar Lantarki

Mun samu rahoton cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya caccaki gwamnatin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya caccaki tsohon shugaban kasar ne dangane da badakalar wutar lantarki da kawowa yanzu taki ci taki cinyewa fadin kasar nan.

Shugaba Buhari dai ya caccaki tsohon shugaban kasar ne dangane da Dalar Amurka Biliyan 16 da ya batar wajen aikace-aikacen wutar lantarki yayin gudanar da gwamnatin sa ba tare da 'yan Najeriya sun ribaci wani kaso na aikin ba.

Shugaba Buhari ya caccaki tsohon Shugaban Kasa Obasanjo akan rashin Wutar Lantarki
Shugaba Buhari ya caccaki tsohon Shugaban Kasa Obasanjo akan rashin Wutar Lantarki

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari bai kama suna yayin gabatar da jawaban sa, sai dai kausasa harshen sa bisa ga yadda wani tsohon shugaban kasa ke tinkaho da bugu kirjin gwamnatin sa ta dabbaka aikace-aikace na makudan kudi domin gyaran wutar lantarki.

KARANTA KUMA: Ba bu lallai Najeriya na da halin biyan Basussukan ta - IMF

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya yi wannan jawabai ne a fadar sa ta Villa yayin karbar bakuncin tawagar magoya bayan sa wanda shugaban hukumar Kastam, Kanal Hameed Ali ya jagoranta.

A kalaman shugaba Buhari, "Ina wutar lantarkin take sabanin da wani tsohon shugaban kasa ke ci gaba da faman tinkaho na batar da sama da Dalar Amurka Biliyan 15 wajen gyaran ta a yayin gudanar da gwamnatin sa."

A shekarar 2008 da ta gabata, majalisar wakilai ta bayyana yadda aka yi asarar $16bn wajen gyaran wutar lantarki karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Obasanja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng