Buhari ya yabi Abacha, ya ce duk abinda za a fada a kan sa, ya yi rawar gani

Buhari ya yabi Abacha, ya ce duk abinda za a fada a kan sa, ya yi rawar gani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba da ayyukan da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Sani Abacha ya yi musamman a fannin gine-gine da shimfida tituna.

Shugaba Buhari ya yi wannan yabo ne a yayin da ya ke jawabi a fadar Aso Villa a lokacin da ya ke tarbar tawagar kungiyar magoya bayan sa karkashin jagorancin shugaban hukumar hana fasakwabri (kwastam), Ahmed Ali.

Buhari ya kuma ce duk irin kallon da wasu ke yiwa Abacha, ya kamata a tuna cewa wasu shugabanin farar hula da suka zo bayan shi sun kashe mukuden biliyoyi a kan ayyukan gine-gine amma babu wani abinda suka tabuka.

Shugaba Buhari ya yabi Abacha, ya zayyana wasu muhimman ayyuka da ya yi
Shugaba Buhari ya yabi Abacha, ya zayyana wasu muhimman ayyuka da ya yi

KU KARANTA: Buhari ya kalubalanci Obasanjo a kan kashe $16bn a fanin wutan lantarki

A wata magana da Buhari ya yi da ake tunanin da Obasanjo ya keyi, Buhari ya ce: "Kun san cewa wani tsohon shugaban Najeriya ne ya lalata layyukan dogo amma yana ta yawo yana cika baki cewa ya kashe $15 biliyan a fanin samar da wutan lantarki, shin ina wutan lantarkin da aka samar? ina wutan lantarkin da aka samar?"

Shugaban kasan kuma ya yi magana kan yadda gwamnatocin baya ke samun mukuden kudade daga siyar da danyen man fetur amma a halin yanzu farashin ya fadi, shugaban ya yi juyayin yadda gwamnatocin bayan suka kasance cikin bashi a maimakon yiwa Najeriya tanadi a baitil mali.

Shugaba Buhari ya cigaba da cewa, "Kun fi ni sani cewa mafi yawancin titunan da muka gina a lokacin PTF suna nan ba'a taba yi musu gyara ba. Ko wane irin ra'ayi ka ke dashi game da Abacha, na amince inyi aiki dashi da hukumar PTF kuma mun gina tituna daga zuwa Fatakwal - Onitsha - Benin - da sauransu ... Bayan haka munyi gine-gine a jami'o'i, ma'aikatu, asibitoci da sauransu."

Shugaban kasan ya yi kira ga yan Najeriya sun bayar da hadin kai a turu a gina Najeriya don bamu da wata kasar da tafi wannan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel