Dalilin da yasa bazan dawo majalisa a yanzu ba - Melaye
- Ciyaman na kwamitin majalisa akan harkokin birnin tarayya, Sanata Dino Melaye, a jiya ne ya bayyana cewa bazai samu damar komawa aiki a majalisa ba domin bashi da isashen karfi a jikinsa
- Sanatan ya kuma ce ya dawo duk da cewa akwai makiya da suka yi kokarin rufe masa baki daga fadin maganganu game da rashin adalci na siyasa da kuma bata suna
- Melaye wanda suka samu ‘yar hatsaniya tsakaninsa da ‘Yan Sanda game da zargin da suke masa da na bawa ‘yan ta’adda bindigogi, wanda hakan yayi sanadiyar kwanciyar sa asibiti
Ciyaman na kwamitin majalisa akan harkokin birnin tarayya, Sanata Dino Melaye, a jiya ne ya bayyana cewa bazai samu damar komawa aiki a majalisa ba domin bashi da isashen karfi a jikinsa.
Sanatan ya kuma ce ya dawo duk da cewa akwai makiya da suka yi kokarin rufe masa baki daga fadin maganganu game da rashin adalci na siyasa da kuma bata suna.
Melaye wanda suka samu ‘yar hatsaniya tsakaninsa da ‘Yan Sanda game da zargin da suke masa da na bawa ‘yan ta’adda bindigogi, wanda hakan yayi sanadiyar kwanciyar sa asibiti, inda ya gurfana a gaban kotu akan gadon asibiti.
KU KARANTA KUMA: Baka tare da mu – Ciyaman na APC ya caccaki ministan Buhari
A wani sako da aka aikawa majiyarmu ta hanyar sadarwa ta watsapp, sanatan yayi godiya ga mutanen Najeriya bisa ga iri goyon baya da suka nuna masa sannan kuma yace zai cigaba da fadar gaskiya kota wane hali.
Idan dai bazaku manta ba an sha gwagwarmaya tsakanin Dino da yan sandan Najeriya inda har ya kai shi ga kwanciya a asibiti bayan fadowa da yayi daga motarsu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng