Hukumar sojin saman Najeriya ta kaddamar da atasa’in Operation Ruwan wuta 4 kan yan Boko Haram

Hukumar sojin saman Najeriya ta kaddamar da atasa’in Operation Ruwan wuta 4 kan yan Boko Haram

Hukumar sojin saman Najeriya a yau Laraba ta kaddamar da atasa’in Operation ruwan wuta a kan yn tada kayar bayan Boko Haram a dajin Sambisa da kuma yankunan tekun Chadi.

Babban kwamandan rundunar, AVM IG Lubo, ya bayyana hakan ne a Maiduguri inda sukayi hira da manema labarai akan nasarorin da aka samu a yaki da ta’addancin da ya kankama a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Labo yace an kaddamar da atasa’in ne domin ragargazan mabuyar Boko Haram da kuma hanasu samun sakewa da motsi a cikin dajin.

Ya kara da cewa zasu gudanar da wannan atasa’i ne tare da jami’an rundunar gamayyar Multinational Joint Task Force (MNJTF) domin taimakawa jami’an sojin kasa.

Hukumar sojin saman Najeriya ta kaddamar da atasa’in Operation Ruwan wuta 4 kan yan Boko Haram.
Hukumar sojin saman Najeriya ta kaddamar da atasa’in Operation Ruwan wuta 4 kan yan Boko Haram.

“Yan ta’addan sunyi gaba da mototcin yaki a kasar Nijar kuma muna zargin sun kawo su wajajen iyakan Najeriya.”

Atasa’in zai tabbatar da cewa an ragargaji motocin da wasu kayan yaki saboda kada yan ta’addan suyi amfani da su.”

KU KARANTA: Bankunan Najeriya zasu fara aiki da fasahar CRS

Gabanin sanarwansa, kwamandan Operation lafiya dole, Manjo Janar Nicholas Rogers yace jami’an sojin saman sun gudanar da atasa’in Operation ruwan wuta 3 tsakanin ranan 12 ga watan Disamba da 17 ga watan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng