Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Manchester ya garzaya Makkah don gudanar da Umarah
Taurarin taurarai na mabuga kwallon kafa, wanda ke da dimbin masoya a harkar tamola, Paul Pogba dake taka leda a kuniyar Manchester United ya garzaya kasar Makkah don gudanar da aikin Ummarah Ibadan Allah.
Legit.ng ta ruwaito cikin wani bidiyo da Pogba ya daura yayin da yake gaban Ka’abah, ya bayyana godiyarsa ga Allah game da samun damar gudanar da Umarah, haka zalika ya bayyana farin cikinsa sosai da sosai.
KU KARANTA: Bari yaro bari: Yaron El-Rufai da jikar Isiyaku sun yi kaca kaca da juna
“Wanda ya zo wurinnan ne kadai zai fahimci dadin da nake ji, don haka ina fata ga duk wadanda basu taba zuwa ba, Allah ya basu daman zuwa wata rana, dukkansu. Wuri ne mai kyau, b azan iya fayyce farin cikina da zuwa wajen nan ba, da ikon Allah kuma zaku zo.” Inji Pogba.
Shi dai aikin Umarah ya kasance ana kiransa da suna karamin Hajji, wanda ake yinsa a kowanne lokaci. Yayin da ake yin asalin aikin Hajjin a shekara ta 12 na watan Musulunci, watan ZulHijja.
Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da Pogba ya yi Umarah ba, don a shekarar 2017 ne ya yi Umararsa ta farko a kungiyar Manchester, bayan kammala kakar wasan shekarar. Sauran Musulmai da suke zuwa Umarah sun hada da Ribery, Benzema, Anelka.
A shekarar 2016 ne dai Pogba ya dawo tsohuwar kungiyarsa, Manchester United daga kungiyar Juventus, inda aka siye shi akan kudi Yiro miliyan 105.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng