Ba bu lallai Najeriya na da halin biyan Basussukan ta - IMF

Ba bu lallai Najeriya na da halin biyan Basussukan ta - IMF

A ranar Litinin din da ta gabata ne cibiyar kula da harkokin kudi ta duniya watau IMF (International Monetary Fund) ta bayyana damuwar ta dangane da tattalin arziki na kasar nan ta Najeriya.

Cibiyar ta bayyana cewa, tana tantamar kasar Najeriya ba ta da hali na sauke nauyin basussukan dake kanta, inda ta nemi gwamnatin tarayya akan ta kara kaimi wajen samar da hanyoyin kudaden shiga a cikin kasar.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, cibiyar ta bayyana hakan ne a yayin gabatar da bincike na al'amurran tattalin arziki da suka shafi yankin Afirka, wanda ya bayyana yadda nauyin bashi ya yiwa mafi akasarin kasashen yankin katutu.

Ba bu lallai Najeriya na da halin biyan Basussukan ta - IMF
Ba bu lallai Najeriya na da halin biyan Basussukan ta - IMF

Jagoran wannan cibiya na reshen Najeriya, Amine Mati, ta bayyana yadda adadin kasashe masu katutun bashi ke ci ga da hauhawa a yankin Afirka, inda adadin su ya tumfaya daga 6 zuwa 15 a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018.

KARANTA KUMA: An nada sabbin Dagatai 77 a jihar Kaduna

Amine ya bayyana cewa, ya kamata Najeriya ta yi hobbasa wajen bunkasa tattalin arzikin ta ta hanyar samar da hanyoyin samar da kudaden shiga a cikin kasar.

Wannan lamari shi zai fitar da kasar ta Najeriya daga cikin kasashen da ake tantamar halin su wajen sauke nauyin basussukan dake kansu kamar yadda Mati ya bayyana.

Legit.ng ta fahimci cewa, zuwa ranar 31 ga watan Dasumbar 2017, nauyin bashin dake kan Najeriya ya kai kimanin N21.73 sabanin yadda yake a N12.12 a ranar 30 ga watan Yunin 2015.

A na ta bangaren shugaba ta hukumar kula da bashi ta Najeriya, Patience Oniha, ta bayyana cewa gwamnatin kasar nan tuni ta zage dantsen ta wajen samar wa gami da inganta hanyoyin samar kudaden shiga a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng