Wasu ‘yan wala-wala sun fada komar ‘yan sanda, an samu miliyoyin Dalar Amurka a wurin su (Hotuna)
Kwamandan rundunar mayar da martanin gaggawa na hukumar ‘yan sanda (RRS) a jihar Legas, Tunji Disu, ya sanar da nasarar cafke wasu ‘yan wala-wala a garin Legas.
‘Yan wala-walar na amfani da ,yan dabaru wajen raba mutane da kayan su, musamman kudi, ta hanyar sajewa da fasinjoji a cikin motocin haya.
An samu kudin, Dalar Amurka miliyan $2m, da suka zambaci wani fasinja bayan sun lallaba shi ya zuwa wurin wani boka.
Hukumar ‘yan sanda ta gargadi matafiya das u zama masu tanka tsan-tsan yayin bulaguro da kuma kiyayewa da mu’amala da bakin fuska a cikin ababen hawa.
DUBA WANNAN: Dan Majalisar wakilai ya bankado cushe a kasafin kudin bana
A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar, wani soja a kasar Zambia mai suna Pathias Mwape ya halaka matarsa, Esther mai shekaru 33 bayan ya gano cewa ba shine ainihin mahaifin 'ya'ya ta haifa masa a zaman aurensu ba.
An gano cewa wani maigidansa a wajen aiki ne mahaifin yaran biyu. Lamarin dai ya faru ne a barikin soja na Chindwin da ke Zambia inda marigayiyar matar ta rika soyaya da mai gidan mijin na ta.
Sojan dai ya ji tsegumi a gari ne inda ake cewa ba shine ainihim mahaifin yaransa ba, hakan yasa ya tirke matar tasa wacce jami'an 'Yar sanda ce kuma ta fashe da kuka inda ta tabbatar masa da cewa yaran ba nasa ba ne.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng