Bari yaro bari: Yaron El-Rufai da jikar Isiyaku sun yi kaca kaca da juna
Wani rikici ya barke a tsakanin babban yaron gwamnan jihar Kaduna, Bello El-Rufai da jikar marigayi sheikh Isiyaku Rabiu, Khadija Rabiu, wanda ta kaisu ga yi ma juna tatas da zage zage a shafin kafar sadarwar zamani ta Twitter.
Jaridar News Digest ta ruwaito zage zagen da yaran suka dinga yi bai tsaya a kansu kadai ba, har ta kai ga suna zagin iyayensu da yan uwansu, kai har ma suna aibanta yan uwan juna da suka rigamu gidan gaskiya.
KU KARANTA: Ana tare: Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Filato da Kotu ta daure shi a Kurkuku
Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa Bello ne ya fara zagin uwar Khadija, inda ita kuma ta zage uwarsa, tana cewa mahaifiyarsa ma kilaki ce, ta kara da ikirarin cewa dan uwan Bello da ya rasu a kwananin baya, Hamza, ya mutu ne sakamakon shan giya.
Sai dai shi ma Bello bai yi kasa a gwiwa ba, inda ya bayyana cewa Khadija ta dade tana son ganin Isiyaka Rabiu ya muru, kuma a yanzu ta yi farin cikin mutuwar attajirin Kakanta, saboda ta samu kudin gado.
Da tura ta kai bango sai Khadija ta bayyana ma Bello idan ya yi wasa zata gurfanar da shi gaban Kotu, kuma za ta tuhume shi da laifin bata mata suna, don haka tace ya yi shiga taitayinsa, ga yadda rikicin.
Ga dai yadda fadar tasu ta kasance:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng