Ma’aikaci ya cizgewa wani dan kasar Indiya hakora 7 saboda bai biya shi albashi ba a Minna
Wani ma’aikaci mai shekaru 23, Ismail Yusuf, ya kai hari sannan ya cizgewa ubangidansa hakora da guduma bisa zargin yaki biyansa albashi.
Mai laifin ya amsa cewa ya cizgewa Sattish Kasara, mutumin kasar Indiya sannan kuma shugaban kamfanin Bolaji Drilling dake Minna, jihar Niger hakora bakwai.
Lamarin wanda ya afku a yankin Tunga dake Minna, ya yi sanadiyan day an sanda suka kama Yusuf.
Legit.ng ta tattaro cewa Kasara ya janye albashin Yusuf saboda ya samu labarin cewa ma’aikacin na shirin tafiya jihar Bauchi don ganin iyayeynsa sannan kuma shi ya ji tsoron kada ya ki dawowa aiki.
Majiyarmu ta rahoto cewa Yusuf yace yayi alkawarin dawowa bakin aiki cikin mako guda, inda ya kara da cewa Kasara ya ki biyansa albashi.
“Na roke shi kan ya biyani albashi na don daukar nauyin tafiya na zuwa Bauchi, amma yaki saurarona ko kuma yi mun uzuri; don haka washegari, na je gidansa, na bude kofarsa ta karfin tuwo sannan na ji masa ciwo a kansa da guduma. Cikin haka ne na cizge masa hakora bakwai,” yayi bayani.
Yaron mai shekaru 23 yace yayi aiki da Kasara tsawon shekaru biyar ba tare day a ziyarci iyayensa ba.
“Na kwashe tsawon shekaru biyar ina yiwa mutumin nan aiki ba tare da na ga iyayena ba sannan abun na damuna hart a kai na kasa jurewa. Ba wai alfarma nake nema ba, albashina nace ya bani,” inji shi.
KU KARANTA KUMA: N-PDP: Ba mu ba Shugaba Buhari wani wa'adi ba - Kawu Baraje
Yusuf ya zargi kamfanin da bautar da yan Najeriya, cewa shi kuma ba zai yarda wani ya zo kasarsa sannan ya bautar da shi ba.
Jami’in hulda da jama’a na jihar Niger, Muhammad Abubakar, ya bayyana cewa jami’an yan sanda sun gano guduma da bututu a hannun Yusuf, inda ya kara da cewa za’a kai shi kotu da zaran an kammala bincike.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng