Manyan ‘Yan PDP za su wuce Garin Bayelsa wajen kaddamar da littafin Jonathan
Mun samu labari cewa a Yau Litinin ne ake sa rai Garin Yenagoa da ke cikin Jihar Bayelsa zai dauki jama’a wajen da za a kaddamar da wani littafi da aka rubuta game da mulkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan na shekaru 5.
Watakila yanzu haka Jiga-jigan ‘Yan PDP na kasar sun wuce Babban Birnin Bayelsa wajen kaddamar da littafin na tsohon Shugaban kasa Jonathan wanda ya fito daga karamar Kabila kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Leadership.
Mataimakin Majalisar Dattawa Ike Ekeremadu da Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike da Takwaran sa na Jihar Ekiti Ayo Fayose da sauran manyan 'Yan PDP za su hallara wurin bikin kaddamar da littaffin da Mista Paul Nwankwo ya rubuta.
KU KARANTA: Sakataren yada labaran APC ya soki Gwamnati Buhari ya kuma yabawa Jonathan
Ana kuma sa rai tsohon Mataimakin Shugaban Kasa watau Arch. Namadi Sambo ya halarci taron matsayin babban bako na musamman. Shi kuma Gwamna Nyesom Wike ne mai masaukin baki a taron da za ayi a Birnin Yenagoa.
Mai martaba Alfred Diete Spiff ne Uban taro inda shi kan shi Goodluck Jonathan ake sa rai yana wurin. Marubucin wannan littafi Nwankwo yace ya rubuta littafin ne domin zayyanawa Duniya wasu daga cikin kokarin Shugaba Jonathan
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng