Ana tare: Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Filato da Kotu ta daure shi a Kurkuku

Ana tare: Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Filato da Kotu ta daure shi a Kurkuku

Wasu jiga jigan yan siyasan Najeriya sun kai ma dan uwansu, tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang ziyara a Kurkuku biyo bayan umarnin daure shi da wata babbar Kotun jihar Jos ta bayar, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar yaki da rasha da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ce ta shigar da karar Jang gaban Kotu bisa tuhume tuhumen 12 da suka danganci karkatar da makudan kudade mallakin al’ummar jihar Filato.

KU KARANTA: Karamar magana ta zama babba: An hallaka wani Musulmi saboda ya yanka Saniya

EFCC ta yi zargin Jang ya tafka laifukan nan ne kimanin watanni kadann a karshen wa’adin mulkinsa a shekarar 2015, sai dai bayan an karanto masa laifuka 12 da EFCC ke tuhumarsa dasu akai, sai ya kada baki ya musantasu gabaki daya.

Ana tare: Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Filato da Kotu ta daure shi a Kurkuku
Jang a Kotu

A zaman Kotun da ya gabata ne dai EFCC ta bukaci Kotu da ta daure Jang, da wani tsohon mai kula da kudi dake ofishin sakataren gwamnatin jihar, Yusuf Pam, duba da girman laifin da suka tafka, inda Alkalin Kotun Mai Shari’a Daniel Longji ya aikasu gidan Yari har zuwa ranar 24 ga watan Mayu, kafin ya saurari bukatar bada belinsu.

Rahotanni sun tabbatar da cewar zuwa yanzu Jang ya kwashe kimanin kwanaki biyar a dakinsa dake Kurkukun jihar Filato, wanda hakan ya sanya manyan yan siyasa, yan uwansa da abokan arziki suka dinga safarar hanyar don kai mishi gaisuwa tare da nuna masa ana tare.

Daga cikin wadanda aka hangi keyarsu a gidan yarin sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Jerry Gana, Chris Giwa, Sanatoci, yan majalisun da sauran gaggan yayan jam’iyyar PDP.

Bugu da kari, bakin da suka ziyarci Sanata Jang na yi ma sauran fursunoni kabakin Alheri, inda shi ma zuwa yanzu ya biya ma fursunoni 50 kudin tarar da ake cisu, wanda hakan ya sa aka sallamesu, kuma biya kudin wuta na Kurkukun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng