Wani Jigo a APC yayi Allah-wadai da Gwamnatin Buhari har da neman afuwar Jonathan

Wani Jigo a APC yayi Allah-wadai da Gwamnatin Buhari har da neman afuwar Jonathan

Mun samu labari cewa Wani babba a da Jam’iyyar APC mai mulki yayi tir da Gwamnatin Shugaba Buhari inda har ta kai yana ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan hakurin cire shi daga mulki da APC tayi a 2015.

Wani Jigo a APC yayi Allah-wadai da Gwamnatin Buhari har da neman afuwar Jonathan
APC tace ba ta san da zaman Frank ba bayan ya soki Buhari

Timi Frank wanda shi ne Mataimakin Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC ya aikawa Shugaba Buhari budaddiyar wasika inda ya koka da irin kashe-kashe da barna da kuma rashin adalci na wannan Gwamnatin ta Buhari.

Frank yace Gwamnatin Buhari ta rusa tattalin arzikin Kasar nan ta kuma jefa jama’a a yunwa. Mista Frank yake cewa kuma a lokacin tsohon Shugaban Kasa Jonathan, Najeriya ba haka ta ke ba inda ya yabawa tsohon Shugaban.

KU KARANTA: Ko ‘Yan N-PDP na iya takawa Shugaban kasa Buhari burki a 2019?

Mista Timi Frank dai yace maganar rashawa da satar dukiyar Gwamnati ya karu ne a Gwamnatin nan don haka ya nemi afuwar Jonathan domin ta tabbata gara lokacin sa da wannan lokaci na mulkin Shugaban Kasa Buhari.

Babban ‘Dan APC ya koka da yadda Gwamnatin Buhari ke cin zarafin ‘Yan adawa ba kamar yadda Jonathan ya kyale ‘Yan APC a lokacin sa ba. Sai dai tuni Jam’iyyar APC ta dura kan Timi Frank tace ba ta san da zaman shi ba.

Mai magana da bakin Shugaban Kasa Buhari watau Garba Shehu yace ya kamata ‘Yan Najeriya sun fahimci cewa idan har Shugaba Buhari ya bar kujera PDP za ta cigaba da sata a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel