Kudin da ake kashewa kan jana’iza ya isa a gina makarantu – Tsohon Gwamna Obi

Kudin da ake kashewa kan jana’iza ya isa a gina makarantu – Tsohon Gwamna Obi

- Kwanaki Tsohon GwamnaPeter Obi ya rasa wata ‘Yar uwar sa a Duniya

- Obi sam bai yi facaka da dukiya wajen jana’izar wannan Baiwar Allar ba

- Dr. Obi yace abin da ake barna ya isa a gina makaranta ko wani kamfani

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi ya bayyana cewa babu dalilin kashe makudan kudi kan matattu. An caccaki Gwamnan ne saboda bai yi barnar dukiya wajen birne ‘Yar uwar sa ta da rasu ba shi kuma ya maida amsa.

Kudin da ake kashewa kan jana’iza ya isa a gina makarantu – Tsohon Gwamna Obi
Babu dalilin kashe kudi kan gawa bayan akwai masu rai
Asali: UGC

Babban Limamin Cocin Enugu ya yabawa Peter Obi saboda irin abin da ya nuna na rashin barnar dukiya lokacin da wata ‘Yar uwar sa ta rasu. Shi dai tsohon Gwamnan bai yi facaka da kudi kamar yadda wasu masu hali ke yi ba.

KU KARANTA: Siyasa: wasu manyan PDP na shirin barin Jam'iyyar

Shi dai Peter Obi ya ki karbar kyaututtuka daga Jama’a inda ya nemi a ba shi kudin a hannun sa. Da wannan kudi tsohon Gwamnan na Anambra yace zai gina wani asibiti da zai taimaki Talakawa amma ba a kare a yanka shanu ba.

Tsohon Gwamna Obi yace kudin da Inyamurai ke kashewa wajen birne mamaci da wasu tarkace a mako guda ya isa a gyara Makarantu da dama kuma har a kafa wani katon kamfanin da zai taimakawa mutanen gari kwarai da gaske.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel