2019: Cikin sati uku zamu narke cikin wata jam’iyyar – Jigo a jam’iyyar PDP

2019: Cikin sati uku zamu narke cikin wata jam’iyyar – Jigo a jam’iyyar PDP

Shugabancin jam’iyyar PDP na fuskantarmatsin lamba daga hadakar jam’iyyun Najeriya 36 da kuma tsofin ‘yan jam’iyyar dake cikin APC a kan ta canja sunan ta domin samar da wata jam’iyya da zata fafata da APC a zaben 2019.

Wani bincike da jaridar Punch tta gudanar ya tabbatar da cewar, hadakar jam’iyyu 36 na Najeriya na son PDP ta ajiye sunan tad a alamar ta tare da narkewa cikin wata jam’iyya da ‘yan Najeruya basu kyamar ta. PDP na shirin mika wuya a kan wannan matsin lamba.

Da yawa daga cikin jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar PDP da shugabannin ta sun nuna amanna da wannan zabi tare da bayyana cewar zasu iya sadaukar da PDP domin samun galaba a kan jam’iyyar APC a zaben 2019.

2019: Cikin sati uku zamu narke cikin wata jam’iyyar – Jigo a jam’iyyar PDP
Shugaban jam’iyyar PDP, Uche secondus

Wani jigo cikin jam’iyyar ya shaidawa Punch cewar, mai yiwuwa nan da sati uku ba za a kara jin sunan PDP a matsayin jam’iyya ba, saidai y ace lokaci ya kure da zasu yi maja amma zasu narke cikin wata jam’iyyar tare da ragowar jam’iyyu da wasu kungiyoyi.

DUBA WANNAN: Buhari ya fi Kwankwaso jama'a a Kano - El-Rufa'i

Dakta, Eddy Olafeso, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na yankin kudu maso yamma, y ace manyan ‘ya’yan jam’iyyar PDP da suka koma APC ne, yanzu kuma suke shirin ficewa, a gaba wajen wannan kira.

Kazalika skataren yada labaran jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya shaidawa Punch din cewar rahoton kwamitin tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da zai mikawa jam’iyyar cikin satin da zamu shiga, zai tabbatar ko PDP zata canja sunan ta ko kuma ba zata yi hakan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel