Zargin sayar da naman mutane a wata kasuwa, mahautan sun maida martani da bayanai
- KAsuwar ta masu sayar da nama a jihar Legas take
- Rahoton baya na gwamnati yace ana zargin ana sada jikin mutane da ma karuwanci
- Sarkin kasuwar yace karya ne
Wata kasuwa a Legas da a bayaa aka zarga cewa ana sayar da naman mutane a cikinta wadda har gwamantin jhar ta Legas tace zata rushe kasuwar yanzu tayi kaurin suna, insa sarkin kasuwar ya fito ya karyata hakan da cewa bata suna ne kawai na masu son gaje kasuwar da farfajiyarta.
Alhaji Malomo Baki Yusuf, sarkin kasuwar Falomo, ya ce zargin da ake musu na karuwanci a kasuwar da kananan yara, da ma kuma zargin wai ana sayar da sassan jikin mutane duk karya ne, kawai magabta ke son gaje kasuwar.
A kasuwar dai an sami cinkoso ne da kazanta, lamari da ya kai gwamnati sonta rushe ta sake gida kasuwar cikin tsari, Sarkin Kasuwa kuma yanzu yace suna maraba da lamarin.
DUBA WANNAN: Rikicin makiyaya bashi da alaka da addinanci ko kabilanci
A shekarun baya ma dai, a jihar ta Legas, an kama wani mutum da ake kira Clifford Orji, mai vin naman mutane in ya kama, sassan jikin mutane kuma yakan sayar wa matsafa dake dauka wai jiki ko jini zai iya zama kudi. Jahilci da in an fahimci Physics, Chemistry da Biology ne kadai za'a ga tsabarsa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng