An kuma: 'Yan fashi sun yi mumunar ta'asa a hanyar Kaduna-Abuja

An kuma: 'Yan fashi sun yi mumunar ta'asa a hanyar Kaduna-Abuja

Matafiya da direbobi sun fuskanci tashin hankali mai tsanani yayinda suka fada hannun 'yan fashi a babban titin Kaduna-Abuja. Mutane da dama sun rasa rayyukansu yayinda wasu kuma sun sami rauni inda aka kuma sace wasu daga cikinsu.

Duk da cewa fashin da akeyi a titin ya fara raguwa a kwanakin baya, fashin da ya faru a ranar Asabar din da ta gabata ya kazanta sosai. A yayinda mutane jihar Kaduna ke jefa kada kuri'an zabukan kananan hukumomi su kuma 'yan fashin sun tare hanya suna cin karensu babu babaka.

An kuma: 'Yan fashi sun yi mumunar ta'asa a hanyar Abuja
An kuma: 'Yan fashi sun yi mumunar ta'asa a hanyar Abuja

KU KARANTA: Dubi yadda zaka iya caje 'dan sanda bayan ya tsare ka a hanya ko yazo maka gida - Hukumar 'Yan sanda

A baya, an ruwaito cewa jami'an yan sandan SARS sun gano makircin da yan fashin da kulawa inda har suka garzaya inda abin ke faruwa kuma sukayi kokarin tarwatsa su sai dai hakan bata yiwu ba saboda yawan yan fashin. Wani jami'in dan sanda ya sami rauni sakamakon musayar wuta da sukayi.

Daya daga cikin direbobin da yan fashin suka tsare ya mutu sakamakon harsashi da ta same shi yayin da yan fashin ke musayar wuta da yan sanda. An kuma ruwaito cewa a yayin da ake musayar wutar, wasu motoccin sunyi hatsari inda mutane hudu suka rasu yayinda wasu mutane 10 suka jikkata.

Wani direba ya ce sunansa Babangida wanda fashin ta ritsa dashi ya ce yan fashin sun tare su ne misalin karfe 6.30 na safie kusa da wani kauye mai suna Katari. "Ni ma'abocin bin hanyar Abuja-Kaduna ne. Ina kan hanya ta na zuwa Abuja tare da fasinjoji a mota ta kirar Golf ne kuma wani direba na gaba na," inji shi.

Jami'in hulda da jama'a na Yan sandan Kaduna, ASP Mukhtar Hussaini ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce basu da labarin cewa an sace wasu mutane. "Jami'an SARS sun isa wurin da ake fashin. An kashe wani dan sanda daya da direban mota guda daya," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164