Abubuwa 10 da ya kamata musulmi su kauracewa a watan Ramadana

Abubuwa 10 da ya kamata musulmi su kauracewa a watan Ramadana

iya, na yin azumi a cikin watan Ramadan domin neman kusanci ga Ubangiji da samun lada. A cikin watan Ramadana ana bukatar mai azumi ya kiyaye wasu abubuwa domin samun ribatar ibadar su ta azumi.

Ga jerin wasu abubuwa 10 da malaman addinin Islama suka ce ya kamata dukkan mai azumi ya kiyaye da su.

1. Kiyaye idanuwa ko kallo: Ana bukatar tsarkake zuciya lokacin azumi, a saboda haka akwai bukatar mai azumi ya kiyaye idanuwan sa daga kalle-kalle musamman na mata.

2. Kauracewa shan hayaki: Duk da kasancewar akwai sabanin fahimta tsakanin malaman adddini a kan shan hayaki, dukkan malaman Islama sun amince cewar bai halatta mai azumi ya ke shan hayaki (tabar sigari ko wiwi) ba.

3. Kauracewa shan giya da biki: Addinin Musulunci ya haramta shan giya gaba daya. Shan giya lokacin azumi zunubi be babba. Dole ne mai azumi ya bar giya matukar yana son amfana daga azumin sa.

Abubuwa 10 da ya kamata musulmi su kauracewa a watan Ramadana
Abubuwa 10 da ya kamata musulmi su kauracewa a watan Ramadana

4. Shan ruwa fiye da kima: Duk da ana wuni ba a sha ruwa ba lokacin azumi, an bukaci masu azumi da su guji yin tatul da ruwa bayan shan ruwa(iftar).

5. Kada mai azumi ya zama malalaci: Yin Azumi ba yana nufin musulmi zai zama malalaci ko maras kuzari ba. Akwai bukatar mai Azumi ya kasance cikin kuzari.

6. Bata lokaci a kan abubuwa marasa fa'ida: Ana son mai ya Azumi ya samu kusanci da ubangiji ta hanyar ninka ibada da zikiri.

DUBA WANNAN: An yi jana'izar Falasdinawa fiye da 50 da Sojin Ira'ila suka kashe a rana guda

7. Fada ko nuna kiyayya: Ana son musulmi su nuna kauna da soyayya da kuma sasanta sabani tsakanin su a lokacin Azumi.

8. Yawan Bacci: Matasa kan bata lokaci da daddare a dandin sada zumuntar yanar gizo tare da dadewa suna bacci da safe. Malaman addini na yin kira ga mai azumi da ya yawaita ambaton Allah fiye da komai.

9. Yawan wasa: Akwai bukatar mai azumi ya rage yawan wasa tare da maye gurbin lokacin wasan da na bautar ubangiji.

10. Hirar batsa: Bai kamata baligai suke hira da kan iya motsa sha'awa ba yayin da suke azumi. Kazalika bai halatta mai azumi ya kalli fina-finai dake nuna batsa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng