Ba sabam-ba: Najeriya na duba yiwuwar samar da makamashin Nukiliya na zaman lafiya

Ba sabam-ba: Najeriya na duba yiwuwar samar da makamashin Nukiliya na zaman lafiya

- Najeriya zata samu tashar farko ta samar da makamashin nukiliya a tsakiyar 2020

- Shugaba kuma zababben jami'i na Nigeria Atomic Energy Commission, Simon Pesco Mallam, ya bayyana hakan a taron da aka kammala na 2018 AtomExpo a sochi, Rasha

Ba sabam-ba: Najeriya na duba yiwuwar samar da makamashin Nukiliya na zaman lafiya
Ba sabam-ba: Najeriya na duba yiwuwar samar da makamashin Nukiliya na zaman lafiya

Mallam ya sanar da The Guardian Exclusive :"Mun gama shirin mu tsaf kuma zuwa tsakiyar 2020 ne. Muna fatan zamu samu makamashin haya kuma zamu kara uku ko sama da haka a shekaru 10 masu zuwa. "

Dangane da tambayar cewa ko Najeriya zata hada kai da Rasha ko a'a, yace :" Muna da yarjejeniya da kasar Rasha, amma bamu sa hannun yarjejeniyar kwangila ba tukun. Munsa hannun yanayin aikin, habaka aikin amma babu wata yarjejeniyar kwangilar haya."

DUBA WANNAN: Ana zargin Bukola Saraki da yi wa gwamnati zagon kasa

A game da yaushe makamashin zai fara aiki, yace: "Gaskiya bansan yaushe bane takamaimai,yanda bazaku zo kuce mun karya alkawari ba. Amma dai ku sani cewa ana shirye shiryen, kuma nan da shekaru kalilan zaku ga sakamakon."

Mallam ya musa rahoton cewa Najeriya ta sa hannu yarjejeniya ta biliyoyin daloli.

Wasu jaridun sun ruwaito cewa Najeriya tasa hannun kwangilar dala biliyan 20 da Rasha. Inaso in sanar daku ba gaskiya bane hakan.

Hadin kai kawai muke dashi da Rasha. Kuma muna fatan in komai ya tafi daidai, zamu sa hannun wata kwangilar dasu. Amma bazamu bayyana kwangilar ba, gudun wasu kada su zagaye mu suje kafin mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel