Abinda shugaba Buhari ya tattauna da sakataren kasar Amurka a hirar wayar tarho - Garba Shehu
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana gamsuwarsa game da irin dangantakar da ake tsakanin Najeriya da kasar Amurka a yanzu.
A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, Shugaban kasar ya furta wannan magana ne yayinda sukayi hira ta wayar tarho da sabon sakataren gwamnatin kasar Amurka, Mike Pompeo a jiya Alhamis.
Shugaban kasan kuma ya yi afani da wannan damar don taya sabon sakataren murna kan nadin da akayi masa inji hadimin shugaban kasan.
KU KARANTA: Wata dattijuwa dake sojin gona da kakin soja ta bayyana dalilinta na saka kakin
Shugaba Buhari ya tuna haduwarsa da Mr. Pompeo a lokacin yana jagoran hukumar leken asiri na CIA inda kuma ya mika godiyarsa a kan irin gudunmawar da kasar Amurka ke bawa Najeriya ta fanin tsaro.
Shugaban kasan Najeriyan kuma ya bukaci sakataren kasar na Amurka ya mika godiyar shugaba Buhari ga Donald Trump bisa irin tarbar karamci da ya yi masa a lokacin da kai ziyara White House.
A bangarensa, Sakatare Pompeo ya jadada wa shugaba Buhari cewar alaka tsakanin kasashen biyu zai cigaba da armashi musamman yanzu da ya ke sakataren gwamnatin kasar.
Ya kuma shaidawa shugaba Buhari cewa kasar Amurka a shirye ta ke don cigaba da hadin gwiwa da Najeriya wajen cigaban nahiyar Afrika a fanoni daban-daban da suka hada da yaki da ta'addanci, kasuwanci da inganta rayuwar mutane.
Shugaba Trump ya nada Pompeo ne bayan da sallame Rex Tillerson kwana daya bayan ya kawo ziyara Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng