Dubi yadda zaka iya caje 'dan sanda bayan ya tsare ka a hanya ko yazo maka gida - Hukumar 'Yan sanda

Dubi yadda zaka iya caje 'dan sanda bayan ya tsare ka a hanya ko yazo maka gida - Hukumar 'Yan sanda

Hukumar 'Yansandan Najeriya ta sanar da al'umma cewa suna da damar su caje duk wani jami'in dan sanda kafin su barshi ya shiga gidajensu ko motarsu don yin bincike.

Hukumar Yan sandan ta bayar da wannan sanarwan ne ta shafinta na dandalin sada zumunta na Twitter inda ta kara da cewa daman haka dokar ta tanadar.

Sai dai hukumar ta ce yana da kyau mutum ya gabatar da wannan bukatar ta sa cikin yanayi na mutunci da karamci.

Ashe doka ta baka damar caje 'dan sanda kafin kafin ya shiga gidanka ko motarka?
Ashe doka ta baka damar caje 'dan sanda kafin kafin ya shiga gidanka ko motarka?

KU KARANTA: Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun canja sheka zuwa jam'iyyar SDP a jihar Jigawa

Mutane da dama sun bayyana mamakinsu a kan wannan sanarwan don a ganinsu babu wani jami'in dan sandan da zai bari farar hula a caje shi kafin ya duba gida ko motar wanda ake son gudanar ba bincike a kanshi.

Hikimar wannan dokar dai shine mutumin da za'a duba gidansa ko motarsa ya tabbatar cewa jami'in dan sandan bai dauke da wani haramtaccen abu da zai iya cewa a cikin gidan ko matar ya gano.

A lokuta da dama, wasu mutane da aka kama dauke da wasu ababe kamar miyagun kwayoyi, makamai da wasu makamantansu suna ikirarin cewa jami'an yan sandan ne ke yi musu sharri su saka abin a gidajensu ko motocinsu.

Idan mutane suka fara amfani da wannan damar da doka ta basu, tabbas za'a magance wannan matsalar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel