Wata dattijuwa dake sojin gona da kakin soja ta bayyana dalilinta na saka kakin
Wata mace mai 'ya'ya uku da dakarun Opertion Checkmate na 81 Division suka cafke sanya da kayan sojoji a garin Legas ta fadawa hukumar soji cewa ta sanya kayan ne saboda ta kaucewa biyan kudin mota.
An kama Mrs Grace Ayeni na tare da wasu mutane 13 wanda duk suke yiwa sojin Najeriya sojan gona. Ta ce ta sanya hular sojojin ne saboda masu motar su ki karban kudin mota daga hannunta.
"Albashina a wata N20,000 ne kuma agent yana karbar N5000 daga ciki, ni da yara na uku muke lalaba N15,000. Ba sata na keyi da kayan sojin ba," inji Grace.
KU KARANTA: Allah ya yiwa shugaban wata jarida a Najeriya rasuwa
An gano cewa wasu daga cikin sauran mutanen da aka kama sanya da kayan sojin tsaffin dakarun soji ne da aka kora daga aiki inda wasu daga cikinsu suka ce suna sanya kayan ne don su kaucewa biyan kudin motan.
Wasu kuma da ba tsaffin sojojin ba sunce sun sanya kayan ne saboda su rika aiki a matsayin masu yiwa motoccin 'yan kwatano' rakiya saboda kada jami'an tsaro su kyale motocin su wuce kuma ana biyansu N5,000 ne a kowace mota.
Daya daga cikin wanda aka kama sanya da kayan sojin ya ce shi tsohon jami'in soja ne amma an sallame shi daga aiki bayan ya dauki hutu amma bai dawo a kan lokaci ba a yayin da suke yaki da yan ta'addan Boko Haram. Ya amsa cewa uniform din nasa ne kuma ya san cewa laifi ne ya yi amfani dashi bayan an sallame shi daga aiki.
Hukumar sojin kuma ta cafke wasu da ake zargin yan kungiyar asiri ta Eiye na yayinda suka kaiwa abokan gabansu hari bayan kammala bikin Magbo a unguwar Ikorodu da ke Legas a ranar Laraba da ta gabata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng