Abin kunya: Kwamishinan jihar Borno ya bayyana dalilinsa na raba ma matasa kayan shushaina

Abin kunya: Kwamishinan jihar Borno ya bayyana dalilinsa na raba ma matasa kayan shushaina

A ranar Alhamis 17 ga watan Mayu ne dai rahotanni suka watsu na cewa wani kwamishinan a jihar Borno da ya rasa abinda zai raba ma matasa a matsayin tallafi, ya raba musu kayan shushaina, watau kayan gyaran takalma da gogesu.

Daily Trust ta ruwaito wannan kwamishina ba wani bane illa, kwamishinan ilimi na gaba sa sakandari, Alhaji Usman Jaha Babawo, wanda a yanzu haka yake takarar kujerar dan majalisar wakilai a yankinsa.

KU KARANTA: Ana nan dai jiya Iyau: Gungun yan bindiga sun far ma kauyukan Birgin Gwari guda 4

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito Babawo yana bayyana dalilansa da suka sanya shi ganin dacewar ya raba ma matasan kayan dinkin takalman, inda yace a matsayinsa na dan siyasa mai yawan mu’amala da talakawa, sai daya tattauna da su, kuma su suka bukaci ya raba musu kayayyakin nan.

Abin kunya: Kwamishinan jihar Borno ya bayyana dalilinsa na raba ma mata kayan shushaina
Jaha da tallafinsa

Wani rahoto da ya bulla a daren jiya ya nuna cewa gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima bai ji dadin wannan lamari ba, inda ya ja kunnen kwamishinan tare da nuna masa tsananin abin kunyar da ya janyo ma kansa, gwamnatin jihar da ma jhar gaba daya.

Gwamnan ya tuna ma kwamishinan cewa ma’aikatarsa ce ta yi dalilin fitar da sama da dalibai yan asalin jihar karatu a kasashen Turai, haka zalika ma’aikarsa ce ta aika da dalibai mata su 100 dake karatun fannin likitanci a kasar waje, wadannan dukansu abin alfahari ne, amma sai ya bige yana kunyata kansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel