Zaben Jihar Kaduna: Jam'iyyar APC tayi nasara a kananan hukumomi 18 yayinda PDP tayi nasara a guda hudu

Zaben Jihar Kaduna: Jam'iyyar APC tayi nasara a kananan hukumomi 18 yayinda PDP tayi nasara a guda hudu

- Hukumar zabe na jihar Kaduna KADSIECOM ta bayyana sakamakon zabukanan kananan hukumomin da akayi kwanan nan

- Sakamakon zaben ya nuna cewa jam'iyyar APC tayi nasara a kananan hukumomi 18 yayinda PDP ta lashe hudu kacal

- Hukumar zaben kuma ta bayyana wasu kananan hukumomin da za'a sake yin zabukan saboda kallubalen tsaro da aka fuskanta

Hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Kaduna (KADSIECOM) ta fitar da sakamakon zabukanan kananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a jihar inda jam'iyya mai mulki ta APC ta yi nasara a kananan hukumomi 14, cikin 18 ita kuma PDP tayi nasara a guda hudu.

Jam'iyyar PDP ta sha kaye a zabukan kananan hukumomi da akayi a Kaduna
Jam'iyyar PDP ta sha kaye a zabukan kananan hukumomi da akayi a Kaduna

KU KARANTA: Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun canja sheka zuwa jam'iyyar SDP a jihar Jigawa

A yayin da ta ke sanar da sakamakon zaben a yammacin jiya Alhamis, Ciyaman din KADSIECOM, Dr. Saratu Dikko-Audu ta ce PDP tayi nasara a kananan hukumomin Zangon Kataf, Kachia, Jema'a da Kauru ita kuma APC ta lashe kananan hukumomin Birnin Gwari, Soba, Makarfi, Sanga, Kaduna ta Arewa, Kubau, Zaria, Giwa, Igabi, Ikara, Kudan, Lere, Sabon gari da Kagarko.

Hukumar bata bayyana sakamakon zabe a kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da Chikun ba saboda an samu 'yan tangarda a wasu gundumomi a kananan hukumomin. Za kuma a sake zabuka a kanannan hukumomi guda uku wanda suka hada da Kaura, Jaba da Kajuru.

Kazalika, hukumar ta sanar da cewa za'a sake sabbin zabuka a ranar 2 ga watan Yuli yayinda kansiloli da Ciyamomi da sukayi nasara za su karbi shedar nasarar zaben a hedkwatan hukumar zaben a ranar Asabar mai zuwa.

Ciyaman din KADSIECOM ta ce ba wani sabon abu ta bayyana ba kawai ta tabbatar da sakamakon da mutane suka sani ne tun a wuraren kada kuri'a da akayi a ranar Asabar din da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel