Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun canja sheka zuwa jam'iyyar SDP a jihar Jigawa

Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun canja sheka zuwa jam'iyyar SDP a jihar Jigawa

- Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar Jigawa sun sauya sheka zuwa sabuwar jam'iyyar SDP

- Sunce sun fice daga jam'iyyar na APC saboda irin yadda ake tafiyar da harkokin jam'iyyar a gundumomi da kananan hukumomi

- A yayin da yake karbansu, Ciyaman din jam'iyyar SDP na jihar ya ce nan da lokaci kadan APC za ta zama tarihi a jihar

Wasu jiga-jigan jam'iyya mai mulki ta APC sunyi fatali da tsintsiya a jihar Jigawa, sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar ne a ranar Alhamis 17 ga watan Mayu inda suka ce za su koma jam'iyyar SDP.

Wadanda suka sauya shekan sun hada da dan majalisar tarayya Honarabul Bashir Adamu da tsohon kakakin majalisar jihar jigawa, Honarabul Abdu Dauda da mambobin majalisar jihar da na tarayya tare da wasu shugabanin kananan hukumomi.

Wasu jiga-jigan APC sun canja sheka zuwa jam'iyyar SDP a wata jihar arewa
Wasu jiga-jigan APC sun canja sheka zuwa jam'iyyar SDP a wata jihar arewa

Legit.ng ta gano cewa sabon Ciyaman din jam'iyyar SDP a jihar, Hon. Abba Anas Adamu ya yi jawabi a madadin wadanda suka sauya shekar inda ya ce sun fice daga APC ne saboda irin rashin bin ka'aidoji da akeyi wajen gudanar da zabubuka a kananan hukumomi.

KU KARANTA: Sojoji sun halaka yan ta'adda 11 kuma sun ceto mata da yara 49 a jihar Borno

Abbas, wanda tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ne ya yi ikirarin cewa jam'iyyar na APC ta ware wasu bangarori da jami'iyyar wanda hakan yasa suka yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar.

Abbas ya ce a yayin gudanar da zabuka a gundumomi da kananan hukumomi da aka kammala cikin kwanakin nan, magoya yiwa gwamna biyaya ne kawai ake damawa da su. Hakan yasa ya yi kira ga duk masu kishin jihar Jigawa su hada hannu tare da su cin ceto jihar daga rugujewa.

A yayin da aka tuntubi mai bawa gwamnan jihar shawara kan kafafen yada labarai, Bello M. Zaki ya ce dama duk wadanda suka fice a jami'iyyar 'yan bin yarima a sha kida ne wanda suke son a rika basu mukammai da kwangila, dama hakan ya sa suka baro PDP.

Ya kara da cewa "Gwamnati na musu fatan alheri a duk inda suka nufa"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel