Sojin Najeriya sun sayo sabbin makamai don yakar Boko Haram

Sojin Najeriya sun sayo sabbin makamai don yakar Boko Haram

- Hukumar Sojin Najeriya ta sake sayo wasu makamai daga kasar waje don yaki da ta'addanci

- Makaman da aka sayo sun hada da alburusai, bindigogi, gurneti, nakiya, bama-bamai wasu makamai masu nisan zango

- An karbi makaman ne a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe inda daga nan za'a rabar da su zuwa wuraren da ake bukatarsu

Hukumar sojin Najeriya ta karbi sabbin kayayakin yaki wanda akayi oda daga kasashen waje wanda za'ayi amfani da su wajen cigaba da yaki da 'yan ta'addan Boko Haram da sauran masu aikata miyagun ayyuka a sauran sassan kasar.

Sojin Najeriya sun sayo sabbin makamai don yakar Boko Haram
Sojin Najeriya sun sayo sabbin makamai don yakar Boko Haram

Ciyaman din kwamitin karbar makamai na hukumar sojin, Olufemi Akinjobi ne ya karbi makaman a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Abinda Buhari ya fadawa Tinubu, Osinbajo, da Oyegun a kan zaben jihar Ekiti

Mr. Akinjobi ya kuma ce kwamitin ta yi odar kayayakin gyaran motoccin yaki da sintiri na sojojin.

Makaman da aka sayo sun hada da alburusai, bindigogi, gurneti, nakiya, bama-bamai wasu makamai masu nisan zango.

Ya dai ce an sayo makaman ne daga wata kasa da Najeriya ta kulla hadin gwiwa ne fanin samar da tsaro.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ce jirgin daukan kaya na Aircargo Global ne yayi jigilar makaman daga nan kuma wasu manyan jami'an sojoji suka sanya idanu kan yadda za'a rabar da makaman zuwa wuraren da suka dace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164