Yau za a saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Kaduna na karshe

Yau za a saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Kaduna na karshe

Hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Kaduna (KADSIECOM) ta sanar da cewa an kammalla tattara sakamakon zabukkan kananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a jihar Kaduna.

A gudanar da zabukan ne a gundumomi 225 da ke kanannan hukumomi 23 da ke jihar a ranar Asabar inda akayi amfani da na'ura mai kwakwalwa a karo na farko don yin zabe a Najeriya.

Za'a sanar da sakamakon zabukanan kananan hukumomin jihar Kaduna a yau
Za'a sanar da sakamakon zabukanan kananan hukumomin jihar Kaduna a yau

An samu tangarda a wasu kananan hukumomi guda biyu; Sanga da Jaba inda wasu yan barandan siyasa suka kai hari ofishin hukumar zaben da ke kananan hukumomin wanda hakan yasa aka soke zabukan.

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Fatakwal bayan wani 'dan sanda ya bindige soja har lahira

Harin da yan barandan suka kai ya sanya ma'aikatan zaben suka tsere don su tsira da rayyukansu, hukumar ta ce za'a saka sabbin ranakun da za'a sake zabukan a wadannan kananan hukumomin biyu.

A baya an sa ran cewa za'a bayyana sakamakon zabukan ne bayan kwanaki biyu amma sai yanzu bayan kwanaki biyar ne hukumar ta ce za'a bayyana sakamakon zabukan a yau.

Wata amintaciyyar majiya daga hukumar zaben ta KADSIECOM ta sanar da jaridar Daily Trust a safiyar yau cewa an kammala tattara sakamakon zabukan kuma za'a bayyana wa al'umma a yammacin yau.

"Za mu yiwa manema labarai bayani misalin karfe 6.00 na yammacin yau," inji majiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel