Da dumi-duminsa: An sa labule yanzunnan tsakanin shugaba Buhari dada Ali Modu Sheriff tsohon shugaban PDP

Da dumi-duminsa: An sa labule yanzunnan tsakanin shugaba Buhari dada Ali Modu Sheriff tsohon shugaban PDP

- A baya suna tare a jam'iyyar ANPP, sai dai Sherif din ya koma PDP

- Ya zama shugaban PDP abin da ya raba kan jam'iyyar sosai

- Yanzu yace ya dawo APC kuma ya tuba

Da dumi-duminsa: An sa labule yanzunnan tsakanin shugaba Buhari dada Ali Modu Sheriff tsohon shugaban PDP
Da dumi-duminsa: An sa labule yanzunnan tsakanin shugaba Buhari dada Ali Modu Sheriff tsohon shugaban PDP

Gabanin zabukan 2019, ana sake ganin sauyin sheka daga manyan jam'iyyu a jihohi da dama, wanda hakan ke nuna abin yazi dab.

An gano Sanata Ali Modu Sheriff tsohon gwamnan jihar Borno a ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau, kuma sun saka labule suna wata ganawar sirri.

Wannan bata rasa nasaba da dawowarsa jam'iyyar APC din bayan da ya gagara shugabantar PDp lamari da ya ja shekaru ana cece-kuce a kotu.

DUBA WANNAN: Labarun Hausa da dumi-duminsu, ga shafinmu

Ko a baya an ga tsohon Sanatan na jihar Borno yana gana wa da mataimakin shugaban kasa Osinbajo a Aso Rock a baara.

Yanzu dai ta tabbata dashi za'a dasa a siyasar yankin gabas ta arewa mai fama da rikicin Boko Haram.

Dama dai PDP taki bashi hadin kai ya shugabance ta don zargin ko tsofin abokansa suka turo shi ya ruguza jam'iyyar daga cikin gida.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel