Wani farar hula ya maka hukumar DSS a kotu, ya bukaci a biya shi N500m
Wani ma'aikacin ma'aikatar ilimi na tarayya ya maka hukumar 'yan sandan farar hula DSS a gaban wata babban kotun Abuja inda ya ke bukatar kotu ta kwata masa hakkinsa bisa kama shi da tsare shi da hukumar tayi ba bisa ka'ida ba.
A takardar shigar da karar, ma'aikacin da ya shigar da karar, Stephen Ejembi Ola wanda ya shigar da karar ta hannun lauyansa ya ambacci hukumar ta DSS ta shugaban hukumar, Lawal Daura a matsayin wadanda ya ke gurfanarwa.
KU KARANTA: Dan majalisa ya bawa matasa tallafin akwatunnan wanke takalma, jama'a sun yi murna
A wata rubuttaciyar shaida da matar wanda ya shigar da karar, Mrs Elizabeth Ola ta gabatar a gaban kotu, ta ce jami'an DSS sun kama mijinta ne a ranar 27 ga watan Afrilun 2018 inda ake tuhumarsa da daukan wani aiki ba bisa ka'ida ba.
Ta ce a baya, hukumar binciken ayyukan cin hanci da makamantansu (ICPC) ta yi bincike a kan batun amma ba'a samu mijinta da laifi ba.
"A halin yanzu hukumar na DSS ta ki amincewa iyalan wanda ake tuhumar ko lauyansa ya gana da shi tun bayan da aka tsare shi.
"Hakan yasa na ke rokon kotu ta ayyana kamashi da tsare shi da akayi a matsayin zin zarafin dan adam musamman yadda aka hana shi ganawa da kowa ko kuma amfani da wayarsa da kuma hana shi abinci da ruwa mai kyau tun lokacin da aka kama shi a ranar 27 ga watan Afrilun 2018," kamar yadda matar ta rubuta.
Mai shigar da karar kuma ta roki kotu ta umurci hukumar DSS ta biya N500,000,000 ga wanda ake tuhuma sobada cin masa zarafi da mutunci da matsi da ya sha tun lokacin da aka kama shi ba tare da gabatar dashi a kotu ba.
A halin yanzu ba'a kai ga mika karar ga alkalin da zai yi shari'ar ba saboda haka ba'a tsayar da ranar sauraron karar ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng