Sarkin gari, limamin gari: Kalli yadda Sarki Muhammadu Sunusi ya nemi watan Ramadan
Shi ma mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II ba a barsa a baya ba a kokarin al’umma Musulmai na neman jaririn wata da zai kawo karshen watan Sha’aban, kuma ya shigar da watan Ramadan.
Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani, Anas Saminu Ja’en ne ya daura hotunan a shafinsa na Facebook, inda aka hangi Sarkin a daren Laraba 16 ga watan Mayu yana neman jaririn watan Ramadan
KU KARANTA: Dakarun Sojin kasa sun yi ma mayakan Boko Haram diran mikiya, sun aika da 15 barzahu

Legit.ng ta ruwaito a cikin hoton ana iya ganin Sarki Muhammadu Sunusi tsaye a saman soron babban Masallacin jihar Kano, watau Masallacin gidan sarki, dauke da na’urar hangen nesa a kokarinsana gano watan.
Sai dai da alama Sarkin bai dace da ganin watar ba, musamman idan aka yi duba da jerin jihohin da sanarwar mai alfarma sarkin Musulmi ta sanar a matsayin jihohin da aka ga watan, da suka hada da Maiduguri, Damaturu, Dutse da kuma Fatakwa.

A daren Laraba ne mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya bada sanarwar ganin jaririn watan Ramadan, inda ya umarci al’ummar Musulman Najeriiya da su dauki azumi daga ranar 17 ga watan Mayu, a matsayin 1 ga watan Ramadan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng