Labari mai dadi: Gwamnatin Tarayya ta bada aikin hanyar Kano zuwa Bauchi
A ranar Larabar nan ne data gabata gwamnatin tarayya ta bayar da aikin hanyar data hada jihar Kano zuwa Bauchi, wacce ta tashi daga Magami-Kwajali-Lingi, mai tsawon kilomita 58.9 akan kudi naira biliyan 15.454
A ranar Larabar nan ne data gabata gwamnatin tarayya ta bayar da aikin hanyar data hada jihar Kano zuwa Bauchi, wacce ta tashi daga Magami-Kwajali-Lingi, mai tsawon kilomita 58.9 akan kudi naira biliyan 15.454. Sannan kuma ta bayar da aikin hanyar Abuja zuwa Legas, wacce ta hada Abuja-Keffi-Akwanga-Legas da kuma Makurdi.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari yayi kira ga musulmai da suyi koyi da halayen Manzo a wannan watan
Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Babatunde Fashola, shine ya sanar da hakan ga majalisa, bayan wani taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsara.
Ya ce; "Ina bukatar jaddadawa jama'a cewa akwai titin daya kunshi kilomita 16 wanda ke kan babbar hanyar Legas, sai kuma hanyar mai tsawon kilomita 251.7 wacce ta tashi daga Otukpo zuwa Makurdi - inda ya tashi tsawon kilomita 268.5, inda aka bada aikin akan kudi dala 995,004.95.
"Dalilin a nan shine hanyar Abuja zuwa Keffi, wanda aka bada aikin a shekarar 2015, wanda a yanzu haka an samu kudin aikin hanyar.
"Saboda haka, wannan shine karo na biyu da aka bada aiki ba tare da an samu kudin aikin ba, amma duk da haka zamu bada aikin da sharadin ranto kudi daga Bankin Exim na kasar China, saboda da zarar an kammala aiki na farko, sai mu fara kokarin gabatar da aikin hanyar Makurdi."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng