Leah Sharibu: Akwai rudu cikin sasanci da 'Yan Ta'adda - Lai Muhammad

Leah Sharibu: Akwai rudu cikin sasanci da 'Yan Ta'adda - Lai Muhammad

Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbaci na cewa har yanzu ba ta yi watsi da batun ceto Leah Sharibu, dalibar Dapchi ta karshe dake tsare a hannun 'yan ta'dda na Boko Haram.

Ministan labarai da al'adu na kasa, Alhaji Lai Muhammad, shine ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan an kammala zaman majalisa na mako da aka saba gudanarwa.

Leah Sharibu tana daya daga cikin Dalibai 111 da aka yashe daga makarantar Dapchi dake jihar Yobe tun a ranar 19 ga watan fabrairun 2018.

Leah Sharibu
Leah Sharibu

Legit.ng ta fahimci cewa, duk da gwamnatin tarayya ta samu nasarar ceto ragowar daliban yayin da biyar cikin su suka riga mu gidan gaskiya, 'yan ta'addan sun kekashe akan sako Leah kasancewar ta mabiyar addinin Kirista kuma ta ki amsar Musulunci kamar yadda rahotanni suka bayyana.

KARANTA KUMA: Da amincewar Fadar Shugaban Kasa muka yiwa Kasafin Kudin 2018 Kwaskwarima - Shehu Sani

Ministan ya jaddada cewa, har yanzu a kowace rana ana ci gaba da sasantawa wajen ceto Leah, sai dai sasanci da 'yan ta'adda akwai kalubalai na razani da rudani a cikin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel