Tsakanin Kwankwaso da Buhari a Kano: El-Rufa’I ya bayyana yadda zata kaya a 2019

Tsakanin Kwankwaso da Buhari a Kano: El-Rufa’I ya bayyana yadda zata kaya a 2019

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’I, ya ce kurari da barazanar da wasu jiga-jigan ‘ya’yan siyasa ke yi na ficewa daga jam’iyyar APC ba zai shafi nasarar shugaba Buhari a zaben 2019 ba.

Wasu manyan ‘yan siyasa da suka hada da tsofin gwamnonin jam’iyyar PDP da suka tsallako zuwa APC sun yi korafin cewar ba a damawa das u a al’amuran jam’iyyar tare da yin barazanar ficewa daga cikin ta.

Wadannan manya ‘yan siyasa sun hada da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, na Sokoto, Aliyu Magatakarda Wammako, na Ribas, Rotimi Amaechi, na gombe, Danjuma Goje, da na Kwara, Bukola Saraki.

Tsakanin Kwankwaso da Buhari a Kano: El-Rufa’I ya bayyana yadda zata kaya a 2019
Nasir El-Rufa’i

El-Rufa’I ya bayyana cewar babu wani dan siyasa da yake da tasirin bawa shugaba Buhari matsala a zaben 2019 tare da bayyana cewar Buhari zai lashe dukkan jihohin su a zaben 2019.

El-Rufa’i na wadannan kalamai ne ranar Talata bayan wata ganawa da shugaba Buhari a Abuja.

DUBA WANNAN: Saraki ya nemi taimakon Buhari bayan Sifeton 'yan sanda ya sako shi a gaba da bincike

Shugaba Buhari zai lashe zabe a jihar Kano domin tun shekarar 2003 yake samun nasara a jihar, a dukkan jam’iyyun day a yi takara. Haka kuma zai yi nasara a jihohin Sakkwato, Kwara da Adamawa koda kuwa jiga-jigan ‘yan siyasar sun yanke shawarar ficewa daga APC,” in ji El-Rufa’i.

El-Rufa’I ya kara da cewar babu mutanen Kwankwaso a dubban jama’ar da suka fito domin tarbar Buhari yayin ziyarar day a kai Kano.

Kazalika, El-Rufa’I, y ace akwai bukatar duba korafen-korafen manyan ‘yan siyasar tare da bayyana cewar bai kamata su yi barazanar ficewa daga APC ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel