Wata mata ta fada komar ‘yan sanda bayan azabtar da karamin yaro bisa zargin maita
Wata mata, Charity Iyonetu, mai shekaru 45, ta shiga hannun jami’an hukumar ‘yan sandan jihar Legas bisa zargin ta da azabtar da wani yaro mai shekaru 12 a kan zargin shi da maita.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Edgal Imohimi, ya sanar da hakan a jiya, Talata, yayin da yake gabatar da wasu masu laifi ga manema labarai a shelkwatar hukumar ‘yan sanda ta Jihar Legas dake Ikeja.
Matar, Charity, ta dauko yaron ne daga mahaifar ta dake jihar Imo bayan mahaifin say a yi watsi da lamuran sa bisa hujjar cewar yaron maye ne saboda yana yawan tsokana da fitina a makaranta.
Bayan ta zo das hi Legas sai ta saka shi a makaranta. Saidai ya cigaba da kiriniya irin ta yarinta tare da guduwa daga makaranta wasu lokutan.
A ranar 9 ga watan Mayu ne da misalin karfe 9:00 na safe Charity ta saka wata dorinar dukan dawakai ta yiwa yaron dukan tsiya tare tare da kulle shi a daki bayan tayi masa daurin huhun goro sannan tayi tafiyar ta shago abinta.
DUBA WANNAN: Hotuna jana'izar Falasdinawa fiye da 50 da sojin Isra'ila suka kashe rana gudu
Kuka da ihun neman taimakon da yaron ke yi ne ya saka wani makwabci kiran ‘yan sanda, wadanda suka zo suka karya kofar dakin suka tserar da shi.
Imohimi y ace sun mika matar sashen binciken laifuka na musamman tare da bayyana cewar zasu gurfanar da ita gaban kotu da zarar sun kamala bincike.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng