Uwargidar shugaban kasa ta karbi bakoncin shuwagabannin jam’iyar matan Arewa
A ranar Talata 15 ga watan Mayu ne shuwagabannin kungiyar matan Arewa suka kai ma uwargidar shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, Aisha Buhari a fadar Villa dake babban birnin tarayya Abuja.
Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na Facebook, Buhari sallau ne ya daura hotunan ziyarar da shuwagabannin jam’iyyar matan Arewa suka kai ma Aisha Buhari a ofishinta dake Villa.
KU KARANTA: Adamu Ciroma da Bilyaminu Usman ne kadai ba maciya amana ba – Inji Buhari
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin ziyarar, Aisha ta tattauna da shuwagabannin kan matsalolin dake addabar mata da kananan yara a Najeriya, tare da bukatar kungiyar ta taimakamata a kokarinta na maganin matsalolin.
Ita dai jam’iyyar matan Arewa an kafa ta ne tun a zamanin tsohon Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna, don haka take daga cikin tsofaffin kungiyoyi a nahiyar Arewa
Ga wasu daga cikin hotunan ziyarar:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng