Cikin hawaye da alhini: An yi jana’izar Faladinawa fiye da 50 da Sojin Isra’ila suka yiwa kisan gilla (Hotuna)
Sojojin kasar Isra’ila sun kasha falasdinawa fiye da 50 tare da raunata wasu fiye da 1,000 yayin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da bude Ofishin jakadancin kasar Amurka a Birnin Kudus.
Falasdinawan sun gudanar da zanga-zangar ne a kan iyakar Gaza, saidai sojojin kasar Isra’ila sun so dakile zanga-zangar da daga bisani tayi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa masu yawa tare da raunata dubbai bayan sun gaza shawo kan masu zanga-zangar cikin sauki.
Dangantaka tsakanin Fasdinawa da Isra’ila ta kara lalacewa ne tare da daukan sabon salo bayab shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana Birnin Kudus a matsayin na Isra’ila.
DUBA WANNAN: Gwamnati zata fara karbar kudin harajin sayar da litattafan addini daga kungiyoyi da cibiyoyin addinai
Kasashen duniya, karkashin jagorancin, Majalisar Dinkin Duniya (MDD), sun kada kuri’ar kin amincewa da kudirin Trump na damka Birnin Kudus ga Isra’ila.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng