‘Yan Shi’a sun ce a shirye su ke su mutu domin El-Zakzaky

‘Yan Shi’a sun ce a shirye su ke su mutu domin El-Zakzaky

- Mabiya Shi’a sun cigaba da yin zanga-zanga a Garin Zaria

- ‘Yan Shi’a na nema Gwamnati tayi maza ta saki El-Zakzaky

- Babban Malamin ya dauki fiye da shekarubiyu a tsare yanzu

Mun samu labari na musamman cewa wasu Mabiya Addinin Shi’a sun yi zanga-zanga a Garin Zaria da ke Jihar Kaduna a dalilin babban Malamin su da yake tsare har yanzu a hannun Hukuma.

‘Yan Shi’a sun ce a shirye su ke su mutu domin El-Zakzaky
Mabiya Shi'a sun buduwa Gwamnati wuta a saki El-Zakzaky

Yanzu haka dai Mabiya addinin na Shi’a sun nemi Gwamnatin Najeriya ta saki Shugaban Kungiyar IMN watau Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky wanda ya fi shekaru 2 a tsare. Tun ba yau Mabiya Shi’an ke kokarin zanga-zanga ba.

‘Yan Kungiyar ta Shi’a sun yi zanga-zanga ne a Yankin gadar Kwangila a cikin Garin Zaria a makon nan su na kira ga Gwamnatin Shugaba Buhari ta saki Zakzaky ya dawo gida. Mabiyan Shi’ar sun ce sun shirya mutuwa a wannan tafiya.

KU KARANTA: Hoton Shehin Malamin Shi'a a hannun Jami'an tsaro

Kwanan nan dai ‘Yan Shi’ar da dama sun shiga hannun Jami’an tsaro a lokacin da su ke zanga-zanga domin a saki babban Malamin na su. A makon nan ne dai Gwamnati ta maka Sheikh Zakzaky da mai dakin sa a gaban wani Kotu a Abuja.

Duk da an bada umarni a saki Malamin har yanzu yana tsare. Dazu kun ji cewa Malaman Musulunci na Jihar Kaduna sun yi Allah-wadai da abin da Mai girma Gwamnan Jihar yayi na tsinewa wasu ‘Yan Majalisar Jihar albarka kwanakin baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng