Fatima Ganduje da mijinta Idris sun yiwa wata mai shafin sadarwa na Hausa wankin babban bargo

Fatima Ganduje da mijinta Idris sun yiwa wata mai shafin sadarwa na Hausa wankin babban bargo

- Diyar gwamnan jihar Kano, Fatima Ganduje da mijinta Idris, sun kasance a bakin mutane masu watsa labarai tun lokacin da aka daura masu aure

- Mutane da dama suna ganin cewa shigar da Fatima tayi ya sabawa al’adar hausawa da kuma addinin musulunci

- Fatima da mijinta sun mayar da murtani ga irin wannan zargi da akeyi masu a kafofin sadarwa na yanar gizo

Diyar gwamnan jihar Kano, Fatima Ajimobi da mijinta Idris Ajimobi, dandan gwamnan jihar Oyo, sun kasance a bakin mutane masu watsa labarai tun lokacin da aka daura masu aure, wanda gwamnoni 22 suka halarta.

Mutane da dama suna ganin cewa shigar da Fatima tayi ya sabawa al’adar hausawa da kuma addinin musulunci, musamman na yarda ta sanya kayan masu nuna jiki.

Fatima da mijinta sun mayar da murtani ga irin wannan zargi da akeyi masu a kafofin sadarwa na yanar gizo, duk da cewa daga farko ta dode kunnuwanta game da maganganun duk da mutane akeyi.

Antykwalba ta wallafa hoton Fatima inda kushe yanayin shigarta ta rubuta kamar haka: "Gaskiya anyi asaran kudin sadakan izufi.

"Bari inga wani shegen yazo ya CE mun rayuwarta ne a kyaleta shashashan banza munafukan addini kuma inji wani yace a cikin gida ne bcos i have posted earlier tana cikin mota da Kayan."

Sun mayarwa wata mai suna Auntykwalba da murtani a kafar sadarwa na Instagram, inda Fatima tace “bai yiwuwa kana gulma kana kuma azumi a lokaci daya saia dai ka zabi daya a ciki”.

KU KARANTA KUMA: Komai tsawon lokacin da za’a dauka, sai an hukunta jami’an da suka aikata rashawa - Buhari

Shi kuma mijin nata yace “Mutunci ba’a sayenshi, ba kuma a haihuwar mutum dashi”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng