Kungiyoyin addini zasu fara biyan gwamnati harajin sayar da Qur’ani da Injila

Kungiyoyin addini zasu fara biyan gwamnati harajin sayar da Qur’ani da Injila

Kasar Uganda ta kakabawa kungiyoyin addini biyan harajin sayar sayar da Qur’ani, Injila (Bible) da ragowar wasu litattafan addu’o’I na addini.

Hukumar tattara haraji ta kasar Uganda (URA) ta tilastawa kungiyoyin addinai a kasar biyan haraji a kan sayar da litattafan addini da na addu’o’i.

Saidai kungiyoyin addinai da malamai sun nuna rashin jin dadin su da juyayi a kan wannan sabuwar doka tare da bayyana cewar bai kamata a saka haraji a kan litattafan addini ba saboda suna amfani das u ne domin tsarkake zukatan mutanen kasar.

Kwamishinan URA, Uwargida Doris Akol, t ace tun farko an yi kuskuren rashin saka masu sayar da litattafan addinai cikin masu biyan haraji.

Kungiyoyin addini zasu fara biyan gwamnati harajin sayar da Qur’ani da Injila
Qur’ani da Injila

Yayin mayar da martini a kan wata takardar koke da limamin wata Cocin Uganda, Archbishop Stanley Ntagali, ya aike mata, Doris ta bayyana cewar gwamnati ba zata cigaba da barin kungiyoyin addinai na shigo da littatafai kasar ba tare da biya masu kudin haraji ba.

Archbishop Ntagali, ya yi korafin cewar gwamnatin kasar Uganda ta rike wasu litattafan addini 9,120 da ya shigo das u daga kasar Kenya, saboda bai biya masu haraji ba.

DUBA WANNAN: Dan sanda ya kashe kan sa saboda an yi masa canjin wurin aiki

Kasar Uganda ta ce zata samu karuwar kudin haraji daga wannan sabuwar doka saboda yawan mabiya addinan Musulunci da Kiristanci dake sayen litattafan addini daga kungiyoyin addini.

Kungiyoyi da cibiyoyin addini a kasar sun gaza samar da adadin litattafan addinai da suke sayarwa a shekara domin bawa gwamnati dammar sanin hakikanin kudin haraji day a kamata su biya.

Shugaban wata kungiyar Hadaka ta addinai a kasar, Mista Joshua Kitakule, ya bayyana cewar duk da batun biyan harajin ba wani abun damuwa bane, kuskure ne ga gwamnatin kasar ta kakaba harajin kasha 18% a kan litattafan addini saboda a cewar sa ba don samun riba ake sayar das u ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel