Mataimakin Shugaban Kasa ya tsarkake Kashe-Kashen jihar Benuwe daga duk wani Tuggu
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi watsi da ikiraran dake yaduwa na cewa kashe-kashe na afkuwa ne a jihar Benuwe a sakamakon wata kullalliyar manufa ta kawar da wasu adadin mutane daga doron kasa.
Osinbajo ya bayyana cewa, babu wata manufa ta tuggu cikin kashe-kashe da zubar da jinin al'umma dake faman afkuwa a jihar Benuwe.
Jaridar ta Punch ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ganawar sa da masu ruwa da tsaki na al'ummar jihar yayin ziyarar aiki da ya kai a fadar gwamnatin dake birnin Makurdi.
Yake cewa, gwamnatin tarayya ta dukufa wajen tabbatar da gaskiyar wannan lamari ta hanyar sake gina yankunan da suka zagwanye a fadin kasar nan sakamakon ta'addanci.
KARANTA KUMA: Ba kai kadai ne wanda ya tsarkaka daga gurbatancin rashawa ba a Najeriya - Dogara ga Buhari
Ya ci gaba da cewa, fushin da al'ummar jihar suka nuna yayin ganawar su tana tafe ne da gamsashiyar hujja wanda zai sanya gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a kasar nan.
Mataimakin shugaban kasar ya bayar da tabbaci inda ya jaddada cewa, gwamnatin kasar nan ba za ta gushe ba ba tare da bankado tushe da silar wannan rikici tare da magance sa a kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng