Adamu Ciroma da Bilyaminu Usman ne kadai ba maciya amana ba – Inji Buhari

Adamu Ciroma da Bilyaminu Usman ne kadai ba maciya amana ba – Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wasu manyan mutane biyu da ya shedesu a matsayin nagartattun mutane da ba su ci amanan al’ummar Najeriya ba a lokacin da suke rike da madafan iko a kasar nan.

Buhari ya bayyana hake ne a yayin ziyarar da ya kai jihar Bauchi a makon da ta shude, inda yace a zamanin da yayi mulkin Soja a shekarar 1985, yana cikin kuruciya ne, don haka ya dinga daure mutanen da yake ganin sun ci amanar Najeriya.

KU KARANTA: Jerin Kamfanoni guda 50 da Najeriya ta baiwa kwangilar hakar danyen mai a shekarar 2018

Jaridar Aminiya ta ruwaito Buhari yana fadin haka ne a lokacin da yake kaddamar da kayan noma da gwamnatin jihar ta sayo ma manomanta, taron da ya gudana a filin wasa na Tafawa Balewa.

Adamu Ciroma da Bilyaminu Usman ne kadai ba maciya amana ba – Inji Buhari
Adamu Ciroma da Bilyaminu Usman

“Na kai mutane da dama kurkuku, tun daga shugaban kasa Shagari zuwa Ministocinsa na kai su kurkun kiri-kiri na ce sun yi laifi, sun ci amanar alumma. Duk wanda ya ci ya amayar, mutum biyu suka fidda Najeriya kunya, da marigayi Bilyaminu Usman, Allah Ya jikansa, da Malam Adamu Ciroma, da har yanzu yana da rai.

“wadannan mutanen sun rike amana, ba a same su da laifi ba, to karshenta yadda zamani yake ni ma aka kamani aka tsare ni, wadanda sukayi abin da suka ga dama, aka maida musu abin da suka dauka, sai gobe lahira Allah zai sake wannan shari’a.” Inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Bilyaminu ya yi karamin minista a gwamnatin Shagari, yayinda Adamu Ciroma ya yi Gwamnan bankin tarayya, ya kuma yi minista.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel