Murna ta koma ciki: Gwamnatin tarayya ta umurci kotu ta janye belin Dino Melaye

Murna ta koma ciki: Gwamnatin tarayya ta umurci kotu ta janye belin Dino Melaye

A yau Laraba ne gwamnatin tarayya ta umurci babban kotun tarayya da ke zamanta a Maitama Abuja ta janye belin da ta bawa Sanata Dino Melaye mai wakiltan yankin kogi ta yamma a majalisar dattawa.

Gwamnatin ta bukaci a janye belin ne saboda rashin gurfanar sanatan a gaban kotun yayin da aka fara sauraron shari'arsa inda ake tuhumarsa da aikata laifuka biyu wanda ofishin Alkalin Alkalan Najeriya ta shigar na yiwa 'yan sanda karya.

An dai gurfanar da Melaye ne a gaban kotun inda ake zarginsa ta yiwa Hukumar Yansanda karya inda yayi ikirarin babban mai tsaron gwamnan jihar Kogi Mr. Edward Onoja David, ya aiko wasu don su kashe shi a ranar 15 ga watan Afrilun 2017.

Murna ta koma ciki: Gwamnatin tarayya ta umurci kotu ta janye belin Dino Melaye
Murna ta koma ciki: Gwamnatin tarayya ta umurci kotu ta janye belin Dino Melaye

Kamar yadda ya ke a karar da hukumar Yan sanda suka shigar a ranar 31 ga watan Janairun 2018, bincike ya nuna cewa Dino Melaye ya sharara karya ne kawai don ya yi wa wasu mutane sharri.

KU KARANTA: Allah yayi: Kotu ta bayar da belin Dino Melaye kan wasu makuden miliyoyi

Melaye ya fadawa tsohon dan gwamna jihar Kogi, Abubakar a wata hirar waya da sukayi, yadda ya shirya makircin kulla wa Mr Edward Onoja David sharri na cewa shine ya shirya makircin yadda kashe shi.

Sai dai a lokacin da kotu ta karanta karar domin a fara shari'a a ranar 16 ga watan Mayu, lauyan gwamnati, Mr Labaran Shuaibu ya bukaci kotu ta janye belin da aka bawa Dino Melaye saboda ya ki hallartar sauraron karar nasa a kotu.

Lauya mai shigar da karan ya kuma bayar da zabin cewa kotu ta tiso keyar wanda ya tsaya wa Dino Melaye don ya bayar da dalili gamsashe ko kuma a tura shi gidan yari.

Ya fadawa kotu cewa gwamnatin tarayya ta tanadar da shedu guda hudu wanda za suyi sheda a kan Dino Melaye.

A bangarensa, lauya mai kire Dino Melaye, Ricky Tarfa ya zargi gwamnatin tarayya da boye wasu muhimman abubuwa game da binciken.

Bayan sauraron bangarorin biyu, alkaliyar kotun, Olasumbo Goodluck ta amince da cewa dole ne wanda ake tuhumar ya hallarci kotu ko kuma wanda ya tsaya masa ya gurfana tare da takardun da ke bayyana dalilin da yasa wanda ake tuhumar ba zai samu hallartan sauraron karar ba.

Kotun ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar Alhamis.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164