Kwankwasiyya Amana: Kwankwaso ya taimake ni – Inji Gwamna Ganduje

Kwankwasiyya Amana: Kwankwaso ya taimake ni – Inji Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa babu shakka tsohon Maigidansa, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taimakeshi sosai a zaman da suka yi ana tare a baya, inji rahoton BBC Hausa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ganduje na cewa sun kwashe sama da shekaru 20 tare da Kwankwaso a tafiyar siyasa, ya kara da cewa: “Mun shafe shekara da shekaru muna siyasa a tare, kuma ya taimakeni, amma ni ma na taimakeshi a zamanmu na tare.”

KU KARANTA: BGwamnatin Buhari ta kulla yarjejeniyar fara aikin layin dogo daga Ibadan zuwa Kaduna

Dayake karin haske ga zargin da magoya bayan Kwankwaso ke yin a cewa wai ya ci amanar tsohon gwamnan, sai Ganduje yace: “A ganinmu wannan ba cin amana bane, sai dai kuma idan shi ne bai fahimci menene cin amana ba, don kuwa bas hi ne ya bani mulkin Kano ba, Allah ne ya bani.”

Kwankwasiyya Amana: Kwankwaso ya taimake ni – Inji Gwamna Ganduje
Kwankwasoda Gwamna Ganduje

Sai dai Gwamnan ba tsaya nan ba, inda ya kara da cewa: “Idan kuma ya dauka cewa ya taimakeni na zaman gwamnan Kano, amma yana min tadiya ta yadda gwamnatina ba za ta samu nasara ba, shi yake nufi da cin amana, to mu bamu kallonsa a matsayin cin amana.”

Daga karshe Gwamnan yace ya fatattaki yan kwankwasiyya daga gwamnatinsa ne sakamakon irin zagon kasar da suke yi ma gwamnatinsa, ya kara da cewa babu wata gwamnati da za ta yarda da masu zagon kasa, ko da Kwankwaso ne kuwa.

Dangantaka ta yi tsami ne tsakanin jiga jigan yan siyasar na jihar Kano ne tun bayan zaben shekarar 2015, inda Kwankwaso ya daga hannun Ganduje don a zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel