Ba kai kadai ne wanda ya tsarkaka daga gurbatancin rashawa ba a Najeriya - Dogara ga Buhari

Ba kai kadai ne wanda ya tsarkaka daga gurbatancin rashawa ba a Najeriya - Dogara ga Buhari

Kakakin majalisar wakilai na Najeriya, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi kadai ba ne ya tsarkaka daga gurbatancin cin hanci da rashawa a fadin kasar nan.

Dogara ya bayyana hakan ne a ranar Talatar da ta gabata yayin shugaba Buhari ke kaddamar da sabuwar shelkwatar hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC a birnin Abuja.

A cewar kakakin, akwai dumbin mutane a kasar nan da suka tsarkaka daga duk wani nau'i na cin hanci da rashawa.

Ba kai kadai ne wanda ya tsarkaka daga gurbatancin rashawa ba a Najeriya - Dogara ga Buhari
Ba kai kadai ne wanda ya tsarkaka daga gurbatancin rashawa ba a Najeriya - Dogara ga Buhari

Yake cewa, cikin ikirarai na shugaba Buhari akan tabbatar da yaki na cin hanci da rashawa a kasar nan hakan ba ya nufin shi kadai ke da wannan gaskiya.

KARANTA KUMA: Yaki da Cin Hanci da Rashawa abu ne mai matukar Wahala - Buhari

A yayin haka kuma Dogara ya yi kira akan inganta jin dadin ma'aikatan hukumar EFCC da hakan zai taka rawar gani wajen kawar masu da rayawar zukatan su wajen aikata barna.

Dangane da sabuwar shelkwatar hukumar EFCC, Dogara ya bayyana cewa hakan yana nuni ne da kwazon gwamnatin tarayya wajen ci gaba da fafata yakokin ta akan cin hanci da rashawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel