Lafiya jari: Abubuwa 6 da mai ciwon ulcer ya kamata ya kiyaye lokacin azumi

Lafiya jari: Abubuwa 6 da mai ciwon ulcer ya kamata ya kiyaye lokacin azumi

Ciwon gyambon ciki (ulcer) matsala ce wadda mutane da dama ke fama da ita, wata kwayar hallita mai tarewa a hanjin mai suna H. Pylori ne ke janyo cutar ko kuma yawan shan magungunan kashe zafin jiki (NSAIDS) wanda sukan sanya fatar da ke lulube hanjin dan adam ta samu rauni wanda hakan kuma ke haifar da ciwon ciki mai radadi, amai dabayan gida tare da jini.

Duk da cewa akwai magunguna da likotoci ke bawa masu fama da ciwon, wani abu mai muhimmanci sosai wajen magance wannan cutar shine lura da irin abincin da mutum ke ci wanda hakan yasa Legit.ng ta kawo muku shawarwarin masana don samun saukin ciwon musamman ga wandanda za suyi azumi.

Lafiya jari: Abubuwa 6 da mai ciwon ulcer ya kamata ya kiyaye lokacin azumi
Lafiya jari: Abubuwa 6 da mai ciwon ulcer ya kamata ya kiyaye lokacin azumi

1) Cin soyayun abubuwa

Mutum ya takaita ciye-ciyen soyayun abubuwa musamman masu maiko sosai da kuma cin duk wani abinci mai dauke da sinadarin acid misali lemun tsami, lemun taba, lemu da innabi da tumatur da makamantansu.

2) Cin abinci mai dauke da yaji da abincin gwangwani

Abinci mai yaji sosai ko kuma abincin gwangwani suna dauke da sinadarai wanda aka sanya don su hana abincin baci da wuri sai dai kuma wannann sinadarin na kara sanya sinadarin acid na cikin dan adam ya karu.

DUBA WANNAN: Ga araha ga amfani: Fa'idoji 6 dake tattare da cin dabino

3) Takaita amfani da suga

Masana sun shawarci masu ciwon ulcer su guji amfani da abinci masu dauke da siga sosai musamman abincin gwangwani da ake sarafawa a kamfanoni.

4) Mugun ci yayin sahur ko bude-baki (iftar) da kuma jinkirta bude-baki

Ana bukatar duk mai fama da ciwon ulcer ya guji cika cikinsa tatul yayin sahur ko bude- baki iftar, kana ba'a son mutum ya jinkirta cin abinci bayan an sha ruwa saboda sinadaren acid da ke cikinsa su samu abincin da za suyi aiki dashi.

5) Gujewa shan taban cigari

Shan taban cigari yana da iloli da yawa ga dan adam da suka shafi huhu da wasu tsokokin jiki, har ila yau, shan tabar na sanya sinadarin acid din cikin dan adam yayi yawa kuma tabar na hana warwakewar raunin da mai ulcer ke dashi a hanjin sa

6) Guji magunguna ciwon jiki musamman ba tare da izinin likita ba

Mafi yawancin magungunan ciwon jiki da ake amfani da su suna cikin wata rukunnin magunguna ne da ake kira turence 'NSAIDS' wanda suna dauke da sinadarin da ke yiwa fatar ciki ko hanjin dan adam illa, saboda haka duk wanda kai azumi ya kamata ya tambaya likitansa ko masana kimiyyan magunguna kafin yayi amfani da magunguna ciwon jiki musamman lokacin azumi.

Abubuwan da masu ciwon ulcer ya dace su ci

1) Mai fama da ciwon ulcer ya kamata ya karkata ne zuwa ga cin abincin da jikin dan adam ke sarrafa su a hankali misali doya, hatsin da ba'a surfe ba, gyda, wake, waken soya, kubewa, cabeji da sauransu.

2) Kayan itatuwa kumar da dabino, ayaba, yalo da sauransu

3) A komawa gashashen nama a maimakon soyaye

4) Idan kuma likitoci sun rubuwata mutum magunguna, sai ya rika sha lokutan da suka umurce shi da sha galibi lokutan sahur ko iftar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: