Abin takaici: Yadda wani Magidanci ya dirka ma diyarsa mai shekaru 15 ciki a jihar Gombe

Abin takaici: Yadda wani Magidanci ya dirka ma diyarsa mai shekaru 15 ciki a jihar Gombe

Idan ba alamun karshne Duniya ba, wannan lamari da mai ya yi kama? Wani dattijon biri ne aka kama a jihar Gombe da laifin zakke ma diyarsa, watau ya mayar da ita matar aure, har sai da ya dirka mata ciki, inji rahoton Daily Trust.

Wannan mutumi mai suna Samaila Zakari mai shekaru 50 ya gurfana a gaba Kotun majistri dake garin Gombe, inda Dansanda mai kara ya bayyana ma Kotu cewa bayani dake Ofishin Yansanda dake garin Deba na cikin karamar hukumar Yamaltu Deba ya nuna cewa Samaila ya aika laifin ne da ranakun 2 da 8 na watan Mayu.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram a wani mummunan samame da suka kai

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da misalin karfe 10 na daren ranakun ne, Mahaifin yarinyar ya dauketa zuwa dakinsa, inda ya kwanta da ta ba tare da izininta ba, a yanzu haka yarinyar na dauke da ciki wata biyu.

Abin takaici: Yadda wani Magidanci ya dirka ma diyarsa mai shekaru 15 ciki a jihar Gombe
Illar fyade

Dansandan, Sufeta Baba Shekari ya bukaci Kotu ta yi duba da sasshi na 390 da 282 na kundin hukunta manyan laifuka ta yanke ma wanda ake kara hukunci, sai dai mahaifin yarinyar ya musanta tuhumar da ake yi masa.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu ne sai Alkali Dorabo Sikam y adage sauraron karar zuwa rabar 21 ga watan Mayu, sa’annan ya bada umarnin a garkame masa mahaifin a Kurkuku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng