Wasu da su kayi wa Buhari fatan mutuwa amma su ka riga sa zuwa gidan gaskiya
Mun kawo jerin wasu jama’a da su ka kirawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari mutuwa saboda tsabar adawa amma kuma sai ga shi sun mutu yayin da shi Shugaban kasar yana nan da ran sa.
Tun lokacin yakin neman zabe dai wasu su ka fara cewa Shugaban kasar bai da lafiya kuma ba zai gama mulki lafiya ba. Shugaban kasar dai yayi ta fama da rashin lafiya bayan hawan sa mulki kuma ya samu lafiya.
Ga dai mutane 3 nan daga cikin su:
1. Aondowase Chia
Tsohon Kwamoshinan Jihar Benuwe a lokacin PDP Chia yana cikin wadanda su kayi wa Shugaban kasa Buhari fatan mutuwa tun kafin ya hau mulki yanzu ya riga mu gidan gaskiya.
KU KARANTA: Wani Minista yayi wa Buhari alkawarin kawo masa Jihar Anambra a 2019
2. Esther Okono
Misis Okono dai wata ‘Yar a-mutun tsohon Shugaban kasa Jonathan ce kuma tayi fata Shugaba Buhari ya mutu tun a 2015. Jim kadan bayan hawan Shugaba Buhari mulki ta rasu.
3. Ben Ubeh
Tsohon Shugaban CAN na Jihar Taraba Ben Ubeh yayi nisa a adawar sa ga Shugaba Buhari har yayi masa fatan mutuwa. Sai dai a bana mota ta buge Ubeh yayi daya-daya ya mutu.
Kwanan nan dai Musa Asake wanda shi ne Sakataren Kungiyar CAN na Najeriya ya rasu. Shi ma dai an ce ya taba cewa Shugaban kasar zai mutu ne a mulki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng