Ba mamaki Tsohon ‘Dan wasan Arsenal ya zama sabon Kocin Kungiyar

Ba mamaki Tsohon ‘Dan wasan Arsenal ya zama sabon Kocin Kungiyar

Ta tabbata dai Arsene Wenger ya tashi daga matsayin da ya rike na tsawon lokaci na mai horas da ‘Yan wasan Kungiyar Arsenal. Har yanzu ana ta ka ce-na ce game da wanda zai maye gurbin Wenger a kulob din na Ingila.

Ga dai jerin Kocin da ake sa rai za su maye gurbin na Arsene Wenger na da ‘yan kwanaki kadan:

Ba mamaki Tsohon ‘Dan wasan Arsenal ya zama sabon Kocin Kungiyar
Ana so Arteta ya gaji Arsene Wenger a matsayin Kocin Arsenal

1. Mikel Arteta

Tsohon Kyafin din na Arsenal yana cikin wadanda ake sa rai za su rike Kungiyar. Sky Sports tace Arteta wanda yayi aiki da Koci Pep Guardiola a Kungiyar Manchester City yana cikin wadanda ake tunani.

KU KARANTA: Ka ji aikin da wasu Sojojin Najeriya su ka yi

2. Julian Nagelsmann

Kocin Kungiyar Hoffeinheim watau Nagelsmann mai shekaru 30 rak a Duniya yana cikin wanda Arsenal ta ke tunanin kawowa. Sai dai da alamu Kulob din na kasar Jamus ba za su saki Kocin da su ke ji da shi ba.

3. Luis Enrique

Jaridun Kasar Ingila sun rahoto cewa abin da zai hana tsohon Kocin Barcelona Enrique maye gurbin Wenger shi ne tsadan albashin sa. Arsenal na neman sabon Koci ne kafin a tafi gasar cin kofin Duniya.

Akwai irin su Max Allegri wanda yace ba zai bar Kungiyar Juventus ba. Haka kuma dai Arsenal na iya duba tsofaffin Kyaftin din su irin su Thierry Henry da kuma Patrick Vieira.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng