2019: Shehu Sani ya lisaffa mazaje 6 dake da aminci kamar shugaba Buhari (jerin sunaye)

2019: Shehu Sani ya lisaffa mazaje 6 dake da aminci kamar shugaba Buhari (jerin sunaye)

- Sanata Shehu Sani ya lisaffa mazaje 6 dake da aminci kamar shugaba Buhari

- Ya ambaci sunan Yakubu Gowon, tsohon shugaban Najeriya daga 1966 zuwaa 1975, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Adamu Ciroma da sauransu

- Sani ya bayyana cewa akwai mutanen kirki a kasar

Sanata mai wailtan Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya lisaffa yan Najeriya dake da aminci kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shehu Sani wanda ya wallafa jerin sunayen a shafinsa na twitter a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu ya kuma jadadda cewa shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari mutum ne mai aminci.

2019: Shehu Sani ya lisaffa mazaje 6 dake da aminci kamar shugaba Buhari (jerin sunaye)
2019: Shehu Sani ya lisaffa mazaje 6 dake da aminci kamar shugaba Buhari (jerin sunaye)

Sani ya ambaci sunan Yakubu Gowon, tsohon shugaban Najeriya daga 1966 zuwaa 1975, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Adamu Ciroma, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari

Ya jadadda cewa akwai mutanen kirki a kasar.

Ga sunayen:

1. Gowon

2. Adamu Ciroma

3. Balarabe Musa

4. Usman Jibrin

5. Yohanna Madaki

6. Aliyu Jamaa

A halin da ake ciki, tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon ya zargi shugabannin da suka zo a bayansa da nemawa cin hanci wajen zama a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel