Wata babbar mota data kwace tare da kutsa kai cikin tasha ta hallaka mutane 10
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane 10 a wata tashar mota mai cunkuson mutane a garin Zaria bayan wata babbar motar tirela ta kwace daga hannun direba ta kutsa cikin tashar.
Wani ganau ya shaidawa gidan Radiyon BBC cewar babbar motar ta tattake mutanen ne bayan ta kutsa kai kai cikin tashar yayin da ta kwace daga hannun direban ta.
Hukumar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar hatsarin da t ace ya faru ne ranar lahadi da daddare. Saidai hukumar bata bayyana adadin mutaanen da suka mutu sakamakon hatsarin ba.
Lamarin ya faru ne a kan gadar garin Zaria, a hanyar zuwa Kano, wurin da jama’a suka mayar tasha ta karfi da yaji duk da kokarin da hukumomi suka yin a ganin cewar tashar ta tashi daga wurin.
DUBA WANNAN: An lalata dubban bindigogi a jihar Zamfara, duba hotunan su
Jama’a a Najeriya na yawan korafin cewar yawancin manyan motoci basu da wadataccen birki. Dalilin da yasa ake samun asarar rayuka duk lokacin da birkin babbar mota ya kasa tsayar da ita.
Ana fargabar cewar adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kan iya karuwa daga 10 da aka bayyana da farko.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng