Son zuciya bacin zuciya: Wani Baban bola ya fuskanci hukuncin Kotu kan satar karfen rodi

Son zuciya bacin zuciya: Wani Baban bola ya fuskanci hukuncin Kotu kan satar karfen rodi

Wata Kotu mai daraja ta daya dake zamanta a Karmo na babban birnin tarayya Abuja ta yanke wani hukunci mai daure kai, ban mamaki da ma ban dariya akan wani matashi dake aikin baban bola a garin Abuja, inji rahoton kamfanin dillancin labaru,NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an gurfanar da baban bolan mai suna Ado Gambo mai shekaru 20 da haihuwa a gaban Kotu ne sakamakon tuhumarsa da laifin sata, inda ake zarginsa da satar wani babban karfen Rodi.

KU KARANTA: Badakalar naira biliyan 6.3: An dage sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar Filato

Dansanda mai shigar da kara, Zannah Dalhatu ya bayyana ma Kotu cewa wani mutumi Mohammed Hamed, mazaunin rukunin gidajen Gwarimpa ne ya kai kara zuwa ofishin Yansanda dake Gwarimpa, a ranar 9 ga watan Mayu.

Son zuciya bacin zuciya: Wani Baban bola ya fuskanci hukuncin Kotu kan satar karfen rodi
Wani Baban bola

Zannah ya cigaba da shaida ma Kotu cewar Gambo ya je wani kangon da Mohammed ke gini, inda ya yi masa sibarnabayyen Rodinsa dake ajiye a wajen da nufin yin aikin ginin da ya sanya a gaba, a cewarsa darajar Rodin ya kai naira dubu hudu.

Daga karseh Zannah yace mai kayan ne ya kama barawon da kansa a lokacin da yake tsaka da kokarin yin awon gaba da karfen, don haka ya bukaci Kotu ta duba sashi na 288 na kundin hukunta manyan laifuka ta yanke ma Gambo hukunci.

Sai dai shi ma baban bolan bai baiwa shari’a wahala ba, inda ya amsa laifinsa, ganin hakan ya sanya Alkalin Kotun Alhaji Abubakar Sadiq ya yanke ma Gambo hukuncin bulala shidda na ta’aziri, sa’annan ya ja kunnensa cewa ba zai samu wannan sassauci ba idan aka sake kawo shi Kotun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng